Shugaban APC na ganawar sirri da Kwankwaso da Tambawal, da ma wasu masu shirin ballewa

Shugaban APC na ganawar sirri da Kwankwaso da Tambawal, da ma wasu masu shirin ballewa

- Adam Oshiomhole ya gana da Kwankaso da Tambuwal

- Tunda ya kama aikin bai samu isasshen bacci ba koda yaushe yanakan hanyar ganawa da mambobin da suka fusata

- Ya roki Tambuwal, Saraki da Dogara dasu daure su zauna a cikin Jam'iyyar

Shugaban APC na ganawar sirri da Kwankwaso da Tambawal, da ma wasu masu shirin ballewa

Shugaban APC na ganawar sirri da Kwankwaso da Tambawal, da ma wasu masu shirin ballewa

Ciyaman na Jam'iyar nan ta APC Adams Oshiomhole yayi wata ganawa da tsohon gwamnan jahar Kano Dr Rabi'u Musa Kwankaso da kuma gwamnan jahar Sokoto Aminu Tambuwal akan daidaito da yakeso a samu saboda fusatar wasu mambobi na Jam'iyar.

Bada jimawa bane da Oshiomhole ya gana da Shugaban majalisa Bukola Saraki da Yakubu Dogara da wasu yan Jam'iyar ta APC a kokarinsa na janyo ra'ayinsu karsu bar jam'iyar.

Yace "Tunda na karbi ofishin nan banyi isasshen bacci ba, kullum ina hanyar tattaunawa da mambobin da suka fusata tun da sassafe".

"Ya gana da Saraki Dogara da kuma Tambuwal inda yake rokon su da karsu bar jam'iyar yanda zasuci gaba da ginata tare"

"Banji dadi ba kasancewar lamarin ya dade ba kafin ya isa teburi na"

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel