Me Obasanjo ke tsoro an sanya masa a kujerarsa a wurin taro?

Me Obasanjo ke tsoro an sanya masa a kujerarsa a wurin taro?

- Kowa yayi mamakin abinda Obasanjo yayi, har da jiga jigan dake gurin zama na gaba a Dakin taron

- Bayan Oramah yayi jawabin maraba, Muchanga da Nelson sai suka je domin lallabar shugaban da ya dawo gaba

- Tsohon shugaban kasan sai ya bi su, inda ya koma gaba. Ya gaisa da jiga jigan inda ya fara da Mustapha zuwa Elrufai, Oramah da Adeosun da sauran su kafin ya zauna

Me Obasanjo ke tsoro an sanya masa a kujerarsa a wurin taro?

Me Obasanjo ke tsoro an sanya masa a kujerarsa a wurin taro?

A taron duk shekara na bankuna da akeyi a Abuja, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yaki zama a gaba, gurin da aka tanada domin shi. Ya zabi ya zauna a baya, tare da sauran wadanda suka halarci taron.

Wannan ya jawo cece ku ce a taron da aka yi a ranar juma'a, 13 ga watan yuli.

Ya zabi ya zauna tare da sauran mutane a maimakon gurin zama a gaba da aka tanadar mishi tare da jiga jigan, a filin taron Transcorp Hilton.

Babu wanda yasan dalilin tsohon shugaban kasan na yin hakan kuma bai yi wa kowa bayani ba.

Kafin isowar Obasanjo, sakataren Gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, gwamna Nasiru Elrufai na jihar Kaduna, Ministan kudi, Kemi Adeosun da Albert Muchanga, kwamishinan hukumar kasuwanci da sufuri na African Union suna zaune a gurin zaman manyan baki.

Ya iso ne yayin da shugaba daraktoci, Benedict Oramah na gabatar da jawabin maraba.

An fara Bude taron ne da bayyana wani adananen tarihin Afreximbank wanda yayi shekaru 25.

Mataimakin shugaban, George Elombi shi yayi jawabin gabatarwa.

Amma da Bronwyn Nelson, Editan CNBC Africa ya je taro Obasanjo daga kofar shigowa, da niyyar kaishi gurin zaman shi, sai tsohon shugaban kasan yaki kuma ya zabi ya zauna a wani gurin zama daga bangaren dama na Dakin taron.

DUBA WANNAN:

Kowa yayi mamakin abinda Obasanjo yayi, har da jiga jigan dake gurin zama na gaba a Dakin taron.

Bayan Oramah yayi jawabin maraba, Muchanga da Nelson sai suka je domin lallabar shugaban da ya dawo gaba.

Tsohon shugaban kasan sai ya bi su, inda ya koma gaba. Ya gaisa da jiga jigan inda ya fara da Mustapha zuwa Elrufai, Oramah da Adeosun da sauran su kafin ya zauna.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel