Wata sabuwa: Gwamnatin tarayya zata fara tantance kafatanin ma'aikatanta sati mai zuwa, duba jadawalin aikin

Wata sabuwa: Gwamnatin tarayya zata fara tantance kafatanin ma'aikatanta sati mai zuwa, duba jadawalin aikin

Shugaban ma'aikatan na kasa, Winifred Oyo-Ita, ta sanar da cewa gwamnatin tarayya zata fara tantance dukkan ma'aikatanta dake ma'aikatu da hukumomin gwamnati daga ranar Litinin 16 ga watan Yulin 2018.

A aikin tanatancewar da za'a kwashe makonni biyu ana yi, ana sa ran za'a tattance ma'aikatu 330,820 dake karabar albashinsu a karkashin tsarin 'Integrated Pay-roll Personnel Information System (IPPIS).

A jawabin da tayi a taron manema labarai data kira a yau Juma'a, Oyo-Ita tace za'a tantance ma'aikatan da suka cike bayanansu ta yanar gizo ne kawai.

DUBA WANNAN: Zaben Ekiti: Jerin sunayen 'yan takara da zasu fafata da kuma jam'iyyunsu

Oyo-ita tace wannan tantancewar da za'ayi zai toshe wasu gibi da ake samu da wasu ke amfani dashi wajen karkatar da kudaden gwamnati.

Wata sabuwa: Gwamnatin tarayya zata fara tantance kafatanin ma'aikatanta sati mai zuwa, duba jadawalin aikin

Wata sabuwa: Gwamnatin tarayya zata fara tantance kafatanin ma'aikatanta sati mai zuwa, duba jadawalin aikin
Source: Twitter

"Wannan tantancewar zata bawa gwamnati damar tabbatar da sahihancin takardun shedan karatun ma'aikatan gwamnati sannan a dauki hotunnan takardun a adana a ma'aijiyar gwamati dake yanar gizo.

"Bayan kammala aikin, ana sa ran za'a warware dukkan matsalolin da ake samu kuma zai kasance dukkan takardun ma'aikata da aka tantance su kasance masu nagarta.

"Za'a fara tantancewar ne a ranar Litinin 16 ga watan Yuli kuma za'a fara ne da ma'aikatun da gwamnati tafi mayar da hankali kansu kuma ana sa za'a kammala cikin makonni biyu." inji Oyo-Ita.

Oyo-ita ta shwarci dukkan ma'aikatan gwamnati su bayar da hadin kai ga masu tantancewar domin duk wanda ba'a tantance shi ya kori kansa daga aikin gwamnati kenan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel