Yanzu Yanzu: Fasto Bakare da Minista Adeosun ba su gana da shugaba Buhari ba – Fadar shugaban kasa

Yanzu Yanzu: Fasto Bakare da Minista Adeosun ba su gana da shugaba Buhari ba – Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta karyata rahotanni dake yawo na cewa Fasto Tunde Bakare na cocin Latter Rain Assembly da ministar kudi, Misis Kemi Adeosun sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa, a yau Juma’a.

Babban mai ba shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.

Ya ce: “Labarai dake yawo na cewa Fasto Tunde Bakare na cocin Latter Rain Assembly da ministar kudi, Misis Kemi Adeosun sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa, a yau Juma’a. Hakan ba komai bane face karya.

"Ministar ta kasance a fadar shugaban kasa saboda taron shekara da kuma bikin cikar bankin African Export-Import Bank (AFREXIMBANK) shekaru 25 wadda za’a gudanar a ranar Asabar a Abuja wanda shugaba Buhari zai halarta.

KU KARANTA KUMA: 2019: Buhari ya nada Dauda Rarara a matsayin daraktan wakoki na kasa

"Ta ci karo ne da Fasko Bakare, wanda ya kawowa shugaban kasar ziyara, sai suka yi gaisuwa. Malamin ya godema ministar bisa samun lokaci da tayi na halartan jana’izar mahaifiyarsa, wanda aka yi a Abeokuta, jihar Ogun a karshen mako.

"Misis Adeosun ta ga shugaba Buhari akalla sau uku a wannan makon, don haka babu bukatar ta sake ganawa da shi a ranar Juma’a.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel