Kungiyar matasan Arewa ta yi gargadi da kakkausar murya akan zaben Ekiti da za’a yi a gobe

Kungiyar matasan Arewa ta yi gargadi da kakkausar murya akan zaben Ekiti da za’a yi a gobe

Kungiyar matasan Arewa ta yi gargadi akan magudin zabe a zaben gwamna da za’ayi a jihar Ekiti a ranar Asabar.

A wata sanarwa daga Yerima Shettima, shugaban kungiyar, ya ce: “Muna ta bibiyar yadda aka ci zarafin martabar damokradiyya da manufofi a jihar Ekiti, ta hanyar amfani da karfi akan gwamna Ayodele Fayose sannan muna burin kaddamar da cewa:

“Abun kunya ne a idon duniya kai hari ga gwamna mai ci wanda miliyoyin talakawan jihar Ekiti suka zaba. Muna Allah wadai da wannan lamari.

Kungiyar matasan Arewa ta yi gargadi da kakkausar murya akan zaben Ekiti da za’a yi a gobe

Kungiyar matasan Arewa ta yi gargadi da kakkausar murya akan zaben Ekiti da za’a yi a gobe

“Bamu ji dadi ba yadda a wannan mataki na tarihin damokradiyar kasarmu ace akwai mutane masu sanya inifam dake barazana ga mutane, ciki harda babban jami’in tsaro da rana tsaka, don kawai su farantawa ubannin gidansu.

KU KARANTA KUMA: Ka binciki yan sanda kan harin Fayose – Sanatocin PDP ga Buhari

"Muna so mu yi gargadi akan lokaci cewa duk wani yunkuri na muzgunawa jam’iyyun adawa a jihar Ekiti a wannan lokaci toh zai haifar da tawaya a zaben 2019 mai zuwa da kuma makomar damokradiyarmu. Don haka wannan baa bun yarda bane."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel