Zaben Ekiti: Gwamna Fayose ya soma ba 'yan jihar cin hancin Naira dubu 3

A daidai lokacin da ya rage duka-duka kasa da awa ashirin da hudu a gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti dake a kudu maso yammacin Najeriya, mun samu cewa Gwamnan jihar mai ci a yanzu Ayodele Fayose ya soma baiwa 'yan jihar cin hancin Naira dubu 3 kowanen su.

Kamar yadda muka samu daga majiyoyin mu da dama, wannan dai bai rasa nasaba da zaben da za'a gudanar a goben inda yake sa ran za su zabi dan takarar jam'iyyar sa ta PDP.

Zaben Ekiti: Gwamna Fayose ya soma ba 'yan jihar cin hancin Naira dubu 3

Zaben Ekiti: Gwamna Fayose ya soma ba 'yan jihar cin hancin Naira dubu 3

Zaben Ekiti: Gwamna Fayose ya soma ba 'yan jihar cin hancin Naira dubu 3

Zaben Ekiti: Gwamna Fayose ya soma ba 'yan jihar cin hancin Naira dubu 3

Zaben Ekiti: Gwamna Fayose ya soma ba 'yan jihar cin hancin Naira dubu 3

Zaben Ekiti: Gwamna Fayose ya soma ba 'yan jihar cin hancin Naira dubu 3

Zaben Ekiti: Gwamna Fayose ya soma ba 'yan jihar cin hancin Naira dubu 3

Zaben Ekiti: Gwamna Fayose ya soma ba 'yan jihar cin hancin Naira dubu 3

KU KARANTA: Da kudin sata Buhari yaci zaben sa a 2015 - PDP

Legit.ng dai ta samu cewa zaben wanda masu fashin baki ke ganin za'a fafata shi ne a tsakanin yan takarar jam'iyyar APC da kuma PDP yanzu haka ya dauki sabon salo.

Wasu daga cikin yan jihar da suka karbi na su sakon na aiken kudin ta wayar su ta salula sun bayyana cewa za su an shi kudin amma kuma za su zabi wanda ransu ke so.

'Yan Najeriya da dama dai na ta tofa albarkacin bakin su game da lamarin inda wasu ke ganin wannan tamkar kokari na lalata demokradiyya a kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel