An shiga cacar baki tsakanin APC da PDP a kan zargin tura N18bn zuwa Ekiti

An shiga cacar baki tsakanin APC da PDP a kan zargin tura N18bn zuwa Ekiti

- A baya, jam'iyyar PDP na jihar Ekiti tayi ikirarin cewa gwamnatin tarayya ta ware wani kaso daga cikin kudaden Abacha saboda ayi amfani dashi a zaben da za'ayi a jihar

- Nan take jam'iyyar APC ta mayar da martani inda tace PDP ta musanta hakan kuma ta kara da cewa PDP na kara samun kwarewa wajen shirya wasan kwaikwayo

- Haka dai jam'iyyun biyu suka cigaba da musayar kalamai masu zafi game da zargin karkatar da kudin

Jam'iyyun siyasar dake da kan gaba wajen takara a zaben gwamna da za'ayi a jihar Ekiti, PDP da APC sun tsunduma cikin musayar kalamai masu zafi game da zargin karkatar da N18 biliyan da PDP tace APC ta ware saboda zaben.

An shiga cacar baki tsakanin APC da PDP a kan zargin tura N18bn zuwa Ekiti

An shiga cacar baki tsakanin APC da PDP a kan zargin tura N18bn zuwa Ekiti
Source: Original

Kamar yadda Vanguard ta wallafa, Mai magana da yawun jam'iyyar APC, Wole Olujobi, ya karyata zargin inda ya kara da cewa wanda bisa ga dukkan alamu wanda ya bayar da sanarwar yana cikin 'maye' ne.

DUBA WANNAN: Abin tausayi: Wasu tagwaye da aka dauka aikin 'dan sanda tare sun mutu rana guda

Tun da farko, dan takarar gwamna a Ekiti karkashin jam'iyyar PDP, Kolapo Olusola, ya zargi gwamnatin tarayya da ware wani kasho cikin $321 miliyan da aka karbo daga cikin kudaden da Abacha ya kai kasashen waje domin yin amfani dashi a zaben da za'a gudanar a gobe Asabar.

Ga wani bangare daga cikin abinda Ojubi ya fadi: "Lere Olayinka dama yana zuka karya kamar yadda mai gidansa gwamna Ayodele Fayose ya saba karyar.

"A sassan kasar nan da kuma kafafen yadda labarai, an san Olayinka da yiwa karya kwaskwarima don masu sauraransu su dauka gaskiya ce yake fadi.

"Duk masu hikima zasu gane cewa Eleka da Olayinka makaryata ne shiyasa suka kwashe mako daya kafin suka kirkiro karyar cewa wai an tura N18 biliyan zuwa jihar Ekiti saboda zabe.

"Sun kirkiro da wannan karyar ne saboda suna son mutane suyi tunanin cewa APC za tayi irin magudin da Fayose ya tabka a 2014 da kudaden da ya karba daga Dasuki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel