Dambazau ya kaddamar da yaki da yan bindiga bayan harin da aka kai kauyukan Sokoto

Dambazau ya kaddamar da yaki da yan bindiga bayan harin da aka kai kauyukan Sokoto

Ritaya laftanal Janar Abdulrahman Dambazau, ministan cikin gidan Najeriya, a ranar Juma’a, 13 ga watan Yuli ya ce gwamnatin tarayya ta jajirce wajen ganin ta saurara tsaro a yankunan da ke fuskantar matsalolin tsaro a kasar.

Dambazau ya kuma sha alwashin cewa gwamnati zata hukunta duk wadanda ke da hannu a hare-haren.

Legit.ng ta rahoto cewa kwanan nan yan bindiga sun kai hare-hare kauyukan Gandi da Tabanni dake karamar hukumar Rabah dake jihar Sokoto, inda suka kashe mutane 39 da kuma raunata wasu tare da mayar da wasu marasa galihu.

Danbazau ya kaddamar da yaki da yan bindiga bayan harin da aka kai kauyukan Sokoto

Danbazau ya kaddamar da yaki da yan bindiga bayan harin da aka kai kauyukan Sokoto

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaio cewa Dambazau ya bayar da wannan tabbaci ne a Sokoto lokacin da ya jagoranci wata tawaga a ziyarar jaje da suka kaiwa Gwamna Aminu Tambuwal.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta zuba N2.5bn daga kudin Abacha a motocin daukar kaya 2 domin tallafawa Fayemi – Dan takarar gwamna a PDP

Ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya damu da lamarin sannan yayi alkawarin kama masu laifin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel