Ekiti 2018: Jirgin sama mai saukar ungulu ya sauka a gidan gwamnati

Ekiti 2018: Jirgin sama mai saukar ungulu ya sauka a gidan gwamnati

Wani Jirgin sama mai saukar ungulu ya sauka a sabon gidan gwamnati, Ayoba Villa, Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti.

Jirgin ya sauka ne a gidan gwamnatin jihar da ranan nan.

Ana zargin cewa jirgin mai saukar ungulu ya kawo kudade ne gana wani gwamnan Kudu maso kudu.

Mambobin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) na ta zarya a gidan gwamnatin don karban kudi.

Suna ta shiga gidan gwamnati ta karamin kofar tsohon ofishin gwamnan.

Ekiti 2018: Jirgin sama mai saukar ungulu ya sauka a gidan gwamnati

Ekiti 2018: Jirgin sama mai saukar ungulu ya sauka a gidan gwamnati

An gano wata mace yar jam’iyyar dake korafin cewa ba’a bata nata kason daga kudin ba.

KU KARANTA KUMA: Babu wanda ya mari Fayose – Yan sanda Babu wanda ya mari Fayose – Yan sanda

Ta ce: “Ba’a bani nawa kason ba alhalin wasu sun karba sau biyu ko.

“Duk wanda ya karbi kudin nan sannan ya ki zabar Eleka ba zai rayu har ya kashe kudin da hannunsa ba.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel