Hukumar DSS ta hana Zakzaky ganin Likita - Kungiyar Shi'a

Hukumar DSS ta hana Zakzaky ganin Likita - Kungiyar Shi'a

Kungiyar daliban mabiya addinin Shi'a a Najeriya wato IMN ta zargi hukumar yan sandan leken asirin Najeriya wato DSS da hana likitoci da iyalan shugabansu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ganawa da su.

A wani jawabi da wani S.I Ahmed ya saki, kungiyar ta bayyana cewa gwamnatin Najeriya na shirin wani kaidin da za'a kullawa Zakzaky domin kashe shi gaba daya.

Yace: "Bisa ga muzahara da tare hanya da mukayi ranan 12 ga watan Disamba 2015, hukumar sojin Najeriya ta kai hari gidan Shaikh Ibrahim Zakzaky kuma suka hallaka akalla yan uwa maza da matan kungiyar dubu daya wanda ya kunshi yar uwarsa mai shekaru 78, da kuma yaransa 3."

Sun harbe shi da niyyar kasheshi amma Allah bai ba su daman haka. A yanzu kuma sun hanashi ganawa da likitocinsa."

A kwanakin baya Wani mumunan rikici ya barke tsakanin jami'an yan sandan Najeriya da yan kungiyar Shi'a a babban birnin tarayya Abuja da ranan nan.

Idanuwan shaida sun bayyana cewa jami'an yan sandan sun watsa wa yan shi'an barkonon tsohuwa ne yayinda suke zanga-zanga a farfajiyar Unity Fountain, kusa da Transcorp Hilton Abuja.

Yan Shi'an sunce ba za su daina wannan zanga-zanga ba muddin gwamnatin shugaba Buhari bata saki shugabansu, Ibrahim El Zakzaky ba.

A jihar Kaduna kuma, sun gudanar da irin wannan zanga-zanga kuma suka kashe jami'in dan sanda guda daya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel