Shehu Sani da Hunkuyi sun fita daga jam'iyyar APC

Shehu Sani da Hunkuyi sun fita daga jam'iyyar APC

Wata bangare na jam'iyyar APC a jihar Kaduna dake yiwa kanta lakabi da APC Akida tare da mambobin kungiyar APC Restoration sun sanar da ficewarsu daga jam'iyyar ta APC baki daya.

Premium Times ta ruwaito cewa kungiyar tace sun yake shawarar ficewa daga APC ne saboda jam'iyyar ta gaza cika alkawurran data dauka wa miliyoyin 'yan Najeriya da suka jefa mata kuri'a.

Kungiyoyin biyu sun bayar da sanarwar ficewarsu ne a wata taron manema labarai da suka kira a garin Kaduna kakashin jagorancin shugaban APC Akida, Mataimaki Maiyashi da Ja'afaru Ibrahim shugaban APC Restoration.

DUBA WANNAN: Abin tausayi: Wasu tagwaye da aka dauka aikin 'dan sanda tare sun mutu rana guda

Kungiyoyin biyu basu bayyana jam'iyyar da zasu koma ba amma sunce suna tattaunawa da wasu jam'iyyoyi da suke ganin akidunsu yazo daya.

Yanzu Yanzu: Magoya bayan Shehu Sani sun fice daga APC

Yanzu Yanzu: Magoya bayan Shehu Sani sun fice daga APC

A cewar Maiyaki, sun gamsu cewa ficewarsu daga APC shine abinda yafi dacewa saboda jam'iyyar bata daukan gyra idan an bayyana mata kurakurenta.

Mr Maiyashi yace sun cinma matsayar kiran taron manema labaran ne bayan tattaunawa da naziri da su kayi da mambobinsu a jihar da ma kasa baki daya.

Sanata Shehu Sani mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya mamba ne da APC Akida kuma ya sha yin barazanar ficewa daga jam'iyyar APC amma bai halarci taron manema labaran ba.

Shugaban ma'aikata na shugaban majalisa Bukola Sarakim Hakeem Baba-Ahmed wanda shima dan APC Akida ne ya fice daga jam'iyyar ta APC kwanakin baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel