Babu wanda ya mari Fayose – Yan sanda

Babu wanda ya mari Fayose – Yan sanda

A ranar Juma’a, 13 ga watan Yuli, rundunar yan sandan Najeriya ta bayyana zargin da gwamnan jihar Ekiti, Mista Ayodele Fayose yayi na cewa jami’anta sun mare shi sannan sun tozarta shi a yayinda suka kai mamaya gidan gwamnatin jihar a matsayin karya.

Kakakin yan sanda, Jimoh Moshood ne ya bayyana hakan a yayin zantawa da yan jaridan gidan talbijin din Channels a shirin rana.

Babu wanda ya mari Fayose – Yan sanda

Babu wanda ya mari Fayose – Yan sanda

KU KARANTA KUMA: Jiga-jigan APC sun ziyarci shugaba Buhari, sun bayyana cikakken abunda suka tattauna (hotuna)

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wata kungiyar matasa a jihar Ekiti, Apapo Odo Ekiti ta yi Allah wadai da Gwamna Ayo Fayose kan yaudarar yan Najeriya da yayi na cewa yan sanda sun kai masa hari.

Kungiyar ta caccaki Fayose akan abun da ta kira a matsayin zubar da martabar jihar a matsayinsa na jagoran mutanen jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel