Saraki ne ya raba kan APC, shi ya kirkiri rAPC, inji wani Sanata

Saraki ne ya raba kan APC, shi ya kirkiri rAPC, inji wani Sanata

Sanata Abdullahi Abdamu mai wakiltar yankin Nasarawa ta yamma kuma tsohon gwamnan jihar Nasarawa ya zargi shugaban majalisa Bukola Saraki da kirkirar bangaren 'yan a wariyya na APC wanda akafi sani da rAPC ko sabuwar APC.

Wasu mambobin jam'iyyar APC da su kayi ikirarin cewa ana yi musu ba dai-dai bane suka kafa sabuwar APC cikin kwanakin nan.

Mr Adamu ya yi ikirarin cewa akwai wasu da su kayi ruwa da tsaki wajen kafa sabuwar APC wanda yace ba za tayi wani tasiri ba. Yace Saraki ba zai iya ficewa daga APC yanzu ba saboda yana tsoron rasa kujerarsa.

Toh fa: Wani Sanata yace Saraki ne ya kirkiri sabuwar APC

Toh fa: Wani Sanata yace Saraki ne ya kirkiri sabuwar APC

DUBA WANNAN: Babbar magana: Jerry Gana ya kaddamar da takararan shugaban kasa a SDP

A wata hira da ya yi da manema labarai a Sakatariyar jam'iyyar a ranar Alhamis, Sanata Adamu yace Saraki da yan korarsa suna iya fice daga APC idan sun ga dama.

Sanata Adamu kuma ya ce, "Wadannan mutanen sun aikata laifuka masu yawa kuma suna son amfani da matsayinsu a jam'iyyar da kuma majalisar tarayya don kaucewa hukuncin da doka za tayi musu.

"Dukkan gumurzu da fafitika da su keyi bashi da wani nasaba da kishin kasa, suna yi ne kawai don kare kansu kuma suna cigaba da kasancewa a APC ne don haddasa fitina."

A yayin da mambobin nPDP suka bukaci zama da shugabanin APC don gabatar da kokensu, Abdullahi yace suna son haddasa fitina ne kawai a jam'iyyar saboda babu wata laifi kwakwara da akayi musu.

Ya yi ikirarin cewa a cikin dukkan mambobin nPDP, Saraki ne yafi samun babban kaso saboda haka koken da suke ne cewa an mayar dasu saniyar ware ba gaskiya bane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel