Zamu sadaukar da takaranmu ga mutum daya domin kayar da Buhari – Sule Lamido

Zamu sadaukar da takaranmu ga mutum daya domin kayar da Buhari – Sule Lamido

Dukkan masu niyyar takaran kujeran shugaban kasa karkashin sabuwar hadakar Coalition for United Political Parties (CUPP) shirye suke da sadaukar da takaransu ga mutum daya wanda zai kawo sauyi ga mutanen Najeriya.

Wannan magana ya fito ne daga bakin tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma dan takaran kujeran shugaban kasa, Sule Lamido, yayinda ya gana da mambobi da shugabannin jam’iyyar PDP a sakatariyarsu da ke Abuja ranan Alhamis, 12 ga watan Yuli, 2018.

Sule Lamido yace jamiyyar All Progressive Congress (APC) sun kidime gabanin zaben 2019. Ya jaddada cewa dukkan yan takaransu sun shirya tsaf domin ajiye takararsu domin daga mutum daya da zai kayar da APC da shugaba Muhammadu Buhari.

KU KARANTA: Na kashe Khadija Oluboyo ne don yin arziki cikin kwana 7 - Saurayinta

Game da cewarsa, ba ya tsoron kowa tunda yayi zaman gidan yari sau 5. Yace Jam’iyyar APC ta fi PDP da take kokarin suka lalacewa kuma a shekarar 2019, yan Najeriya za su tsigesu daga mulki.

Yace: "Yan takaran da ke PDP da gamayyar sun shirya sadaukar da niyyarsu domin rana goben Najeriya. Abin na ban tausayi, yan Najeriya na bani tausayi saboda wasu sun haye kan mulki ba tare da shiri ba.”

“Mutane na mutuwa a ko ina, ana garkuwa da mutane kullum, daga Abuja, Birnin Gwari, Zamfara”

A karshe, yace jam’iyyar PDP ta gaji da jin abubuwan da ke faruwa saboda haka ya zama wajibi ta kwato mulki daga hannun APC.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel