Yanzu Yanzu: Buhari ya ki sa hannu a wasu dokoki hudu da majalisa ta gabatar masa

Yanzu Yanzu: Buhari ya ki sa hannu a wasu dokoki hudu da majalisa ta gabatar masa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli ya bayyana hukuncinsa na kin sanya hannu a wasu dokoki hudu da majalisar dokoki ta gabatar masa.

A majalisar wakilai, hukuncin shugaban kasar na kunshe ne a cikin wata wasika wanda kakakin majalisa, Mista Yakubu Dogara ya karanto a yayin fara zama na yau.

Dokokin sune “Dokar kisan kai bisa kuskure, 2018”, “dokar shirin bayar a bashin noma, 2018”, Dokar kare yara, 2018”, da kuma “Dokar biyan tara a kotu, 2018.”

Buhari ya bayar da dalilansa na kin amincewa da dokokin.

Yanzu Yanzu: Buhari ya ki sa hannu a wasu dokoki hudu da majalisa ta gabatar masa

Yanzu Yanzu: Buhari ya ki sa hannu a wasu dokoki hudu da majalisa ta gabatar masa

Misali, kan dokar kashe mutum bisa kuskure, Buhari ya ce dalilai da dama da aka samar day a sabama kundin tsarin mulkin 1999.

Ya kuma ki amincewa da dokar shirin bayar da bashin noma bisa dalilin cewa majalisar dokoki ta garkame kudin da aka ware don wannan shiri zuwa N50bn.

Shugaban kasar ya bayyana cewa hankalin shi ya fi kwantawa da naira miliyan 100.

KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa za ta bayyana sunayen mutane 200 da suka mallaki dukiyoyi ta hanyar haram

Kan dokar kare yara, Buhari ya bayyana cewa wannan hukuma kawai zata sake wanzar da ayyuka irin na hukumomin da ake dasu ne da ma’aikatar harkokin mata.

Ya ki amincewa da dokar kotun saboda rikitarwa da haifar da rikici a dokoki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel