Abin tausayi: Wasu tagwaye da aka dauka aikin 'dan sanda tare sun mutu rana guda

Abin tausayi: Wasu tagwaye da aka dauka aikin 'dan sanda tare sun mutu rana guda

Garin Minna ya fada jikin jimami saboda bakin cikin rasuwar wasu tagwayen jami'an 'yan sanda da suka rasu sakamakon hatsarin mota a ranar Talata.

Tagwayen yan sandan sun shiga aikin dan sanda a rana daya kuma sunyi farin jini da suna cikin al'umma saboda jajircewarsu wajen gudanar da ayyukansu.

Hawaye sun kwaranya yayin da hukumar yan sanda reshen jihar Neja ta samu labarin rasuwar 'yan biyun.

Abin tausayi: Wasu tagwaye da aka dauka aikin 'dan sanda tare sun mutu rana guda

Abin tausayi: Wasu tagwaye da aka dauka aikin 'dan sanda tare sun mutu rana guda

An ruwaito cewa Hassan da Hussaini sun rasu ne bayan wani direban mota ya fada musu a garin Maitumbi dake kan iyakar Minna.

DUBA WANNAN: Bayan janyewar sojoji, 'yan bindiga sun cigaba da cin karensu babu babbaka a hanyar B/Gwari

'Yan biyun suna kan babur ne lokacin da hatsarin ya faru.

Daya daga cikin 'yan biyun ya kai mukamin Saja yayin da dayan kuma Kofur ne kuma mutane sun musu kyakyawar sheda saboda irin kwazo da jajircewa da suke dashi wajen aiki. Dukkansu biyu suna aiki ne a hedkwatan Yan sanda na Minna.

An gano cewa matar Hussaini ta haifi 'yan biyu cikin 'yan kwanakin nan.

Direban da ya bige su da motarsa kirar Peugeot 206 shima yana asibiti yana karban magani sakamakon raunin da ya samu.

Rahottani sun bayyana cewa direban mai suna Mohammed har yanzu bai farfado ba tun lokacin da aka kwantar dashi a babban asibitin Minna.

Kakakin hukumar 'Yan sanda na jihar, Mohammed Abubakar ya tabbatar da afkuwar rasuwarsu inda yace hatsari ne ya afku.

"Hatsari ce ta faru, a halin yanzu ana gudanar da bincike, idan an kammala binciken zamu san matakin da za'a dauka."

Abubakar kuma yace tuni an bawa iyalansu gawawakinsu saboda ayi musu jana'iza kamar yadda addinin Islama ya tanada.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel