Fadar shugaban kasa za ta bayyana sunayen mutane 200 da suka mallaki dukiyoyi ta hanyar haram

Fadar shugaban kasa za ta bayyana sunayen mutane 200 da suka mallaki dukiyoyi ta hanyar haram

Fadar shugaban kasa ta ce kwanan nan zata wallafa sunayen mutane 200 da suka mallaki dukiyoyinsu ta hanyar rashawa a fadin kasar.

Babban mai ba shugaban kasa shawara akan hukunci, Okoi Obono Obla ya bayyana hakan a jiya a wajen taron kaddamar da sabon na’urar da zata gano kayayyakin haram a kasar wanda wata kungiyar jama’a African Network for Environment and Economic Justice (ANEEJ) ta samar a Abuja.

Obla, wadda ya kuma kasance shugaban kungiyar bincike akan dawo da kayayyakin sata, ya ce kadarorin na a manyan yankuna kamar su Maitama Abuja, suna da alaka da jami’an gwamnati masu ci da na baya.

Fadar shugaban kasa za ta bayyana sunayen mutane 200 da suka mallaki dukiyoyi ta hanyar haram

Fadar shugaban kasa za ta bayyana sunayen mutane 200 da suka mallaki dukiyoyi ta hanyar haram

Da ake kaddamar da na’urar gano kadarorin, yace yaki da rashawa na dukkanin yan Najeriya ne saboda “rashawa ya shafi dukkaninmu.”

KU KARANTA KUMA: Jigon APC a Bayelsa ya fado daga ginin bene mai hawa 2 ya mutu

Daraktan ANEEJ, David Ugolor ya ce na’urar na yanar gizo ne da zai bayar da bayani akan dukiyoyin mutane a kowani yanki na Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel