Jigon APC a Bayelsa ya fado daga ginin bene mai hawa 2 ya mutu

Jigon APC a Bayelsa ya fado daga ginin bene mai hawa 2 ya mutu

Wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress, reshen jihar Bayelsa, Cif Lionel Jonathan-Omo ya rasu.

Jonathan-Omo, mataimakin daraktan yakin neman zabe na Sylva/Igiri a lokacin zaben gwamna na 2016 a jihar ya fado ne daga barandar gidansa mai hawa biyu a Beleu-Pogo na Ogbolomabiri, dake karamar hukumar Nembe na jihar.

Yana hutawa ne a barandar lokacin da ya fara jin jiri. Yana kokarin tashi da taimakon ginshikin dake kusa das hi lokacin day a fado daga ginin bene biyun.

Makusancin sa sun bayyana cewa matarsa c eta Ankara da fadowar nasa bayan ta ji kara daga madafa.

Jigon APC a Bayelsa ya fado daga ginin bene mai hawa 2 ya mutu

Jigon APC a Bayelsa ya fado daga ginin bene mai hawa 2 ya mutu

A take aka kai shi asibiti a jihar inda likitoci suka bayar da shawarar a kais hi asibitin koyarwa na jami’ar Port Harcourt dake jihar Rivers.

KU KARANTA KUMA: Wani Sanata ya nemi a tsige Gwamnan Zamfara Yari daga ofis

An tattaro cewa anyiwa marigayin aiki a lokacin da aka kaishi UPTH amma bai tashi ba bayan aikin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel