Jiya ba yau ba: Irin sukar da Buhari yayi wa Shugaba Jonathan lokacin yana kan mulki

Jiya ba yau ba: Irin sukar da Buhari yayi wa Shugaba Jonathan lokacin yana kan mulki

Idan ba ku manta ba a baya Shugaba Muhammadu Buhari lokacin yana babban ‘Dan Jam’iyyar adawa a Kasar nan ya rika sukar Gwamnatin tsohon Shugaban kasa Goodlcuk Jonathan na Jam’iyyar PDP game da tabarbarewar harkar tsaro a Najeriya.

Jiya ba yau ba: Irin sukar da Buhari yayi wa Shugaba Jonathan lokacin yana kan mulki

Buhari yayi ta sukar Jonathan sai ga shi harkar tsaro na jagwalgalewa a gaban sa

Yanzu an bankado irin kalaman da Shugaban kasar ya rika yi ganin cewa sha’anin tsaro a kasar na nema ya sukurkuce. Ana dai fama da kashe-kashe a wurare da dama wanda wani lokacin Shugaban kasar yace akwai hannun wasu manyan ‘Yan siyasa.

A farkon 2015 kafin ayi zabe, Shugaban kasa Buhari ya koka da kashe jama’an da aka rika yi a Najeriya amma Gwamnatin bayan ba tayi komai ba don ta sa batun zabe ne kurum a gaban ta. Shugaban Kasa Buhari yayi Allah-wadai yace akwai sake a lokacin.

KU KARANTA: Mutanen da su ke shirin fitowa takarar Shugaban kasa daga Arewa

Bayan na Shugaba Buhariyayi alkawarin kare rayukan al’umma idan ya hau mulki inda yace abokan adawa ba za su rika kai mana hari ba. Kwanan nan ne dai aka kashe mutane da dama a wani Kauye da ake kira Tabani da ke cikin Garin Sokoto cikin ruwan sanyi.

A lokacin zaben Gwamnan Jihar Ekiti a 2014, Gwamnati ta aika Jami’an ‘Yan Sanda 7000 wanda hakan ya jawo fushin Jam’iyyar adawa saboda ganin ana tsakiyar rikicin Boko Haram. Yanzu dai za a tura ‘Yan Sanda 30, 000 ne zuwa aikin zaben na Ekiti da za ayi.

Jiya kuma kun ji cewa manyan Malaman addinin Kirista da ke Arewacin Najeriya da ke da jama’a har a irin su Kasar Amurka da Taiwan sun nuna cewa za su marawa tsohon Ministan nan Kabiru Tanimu Turaki bayan ya kara da Shugaban kasa Buhari a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel