Rukunin mutane biyu kacal fayose ke birgewa - Obasanjo

Rukunin mutane biyu kacal fayose ke birgewa - Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya bayyana mamakinsa bisa yadda mutane ke goyon bayan gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose.

A wani sako da aka fitar ta shafin Tuwita na @chief_Obasanjo, Obasanjo ya bayyana cewar Fayose na birge jahilai da wawaye ne kawai.

Obasanjo na wadannan kalamai ne a matsayin martani ga dambaruwar siyasa dake faruwa a Ekiti gabanin zaben gwamna da za a yi a jihar ranar Asabar maj zuwa.

Rukunin mutane biyu kacal fayose ke birgewa - Obasanjo

Sakon Obasanjo cikin harshen turanci

Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya bayyana mamakinsa bisa yadda jama'ar jihar Ekiti suka sake zaben Fayose a matsayin gwamna a shekarar 2014 domin a cewar Obasanjo, Fayose ba shi da wata gudunmawa ta kirki da zai bawa jama'a balle har ya kawo masu cigaba domin har yanzu da wa'adin mulkinsa ya kare babu wani aiki da ya yiwa mutanen jiharsa.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa na tsaya takarar shugabancin kasa - Atiku ya budewa 'yan majalisa cikinsa

An dade ba a ga maciji tsakanin Obasanjo da Fayose, domin ko a kwanakin baya da gwamnati ta fara zargin Obasanjo da kashe dala biliyan $16 domin samar da wutar lanatarki lokacin da yake mulki saida Fayose ya nuna goyon bayan gwamnati a kan ta tuhumi Obasanjo.

An fara zaben Fayose a matsayin gwamnan jihar Ekiti a shekarar 1999 amma kafin ya kai ga karasa zangonsa sai Obasanjo ya sa aka tsige shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel