'Yansandan jihohi: An kai kudurin dokar ga majalisa, gwamnoni na murna

'Yansandan jihohi: An kai kudurin dokar ga majalisa, gwamnoni na murna

- An kai 'yansanda maqura wajen kokarin kare jama'a, don laifukan sunyi yawa

- Kashe-kashe da ma barayin daji sun nuna yansandan tarayya kadai sunyi kadan

- Wasu na ganin 'yansandan jihohi karkashin gwamnoni zai iya kawo yaki na kabilanci

'Yansandan jihohi: An kai kudurin dokar ga majalisa, gwamnoni na murna

'Yansandan jihohi: An kai kudurin dokar ga majalisa, gwamnoni na murna

Majalisar dattijai, a jiya, ta karbi kudurin da zai bada damar kudira dokar da zata bada dama jihohi su kafa nasu 'yansandan, da ma basu makamai, kudiri da a baya an sha kawo shi amma ana fatali dashi saboda tsaro.

Dalilan dai da aka bayar, sun hada da gazawar gwamnatin tsakiya, na kare jama'a musamman masu zama a karkara, wadanda yan ta'adda ke kashe wa babu kakkautawa shekara da shekaru.

A kokarin cika alkawarin sa na gabatar da dokar deputy senate na majalisar Sen. Ike Ekwerenmadu shiya gabatar da takardar.

Ekwerenmadu yana da magoya baya 75 da sukayi ammana da dokar wanda gaba daya adadinsu ya kama 76 har dashi. Wanda yanda da kaso sama da 82 daga cikin 106 na yan majalisar.

Har zuwa wannan lokaci ba'a bayyanawa manema labarai abinda dokar take dauke dashi ba.

Tare da wannan doka yan majalisar sun nemi da a sanya sha'anin tsaro daga jerin da yake a maidashi jerin da yake na lokacin, wanda zai bawa gwamnoni damar iko da yan sandan jahar su.

Shugaban majalisar yayin da yake yiwa abokan aikin sa barka da dawowa daga hutun da sukaje ya bayyana cewa yanzu lokaci ne da zasu yanke hukunci akan tsarin tsaro na kasar nan.

DUBA WANNAN: An janye yansanda daga gidan Ayo Fayose

"Yace munyi magana dangane da sha'anin kashe kashe shin da gangan akeyi ko kuwa maida martani ne, koma dai menene muna gab da kawo karshen abun."

"A matsayin mu na yan majalisa munsan abunda zamuyi akai sannan mu bayyana masu zartarwa abunda zasuyi a sirrance sannan Mun bayyana musu a fili, sannan mu kuma zamusan matakin dauka".

Gwamnoni dai, zasu dara idan aka zartas da wannan dokar, saboda zai basu karfi irin na shugaban kasa.

Tsoron da ake dai, shine amfani da irin wadannan don bangar siyasa, ko kabilanci tsakanin jihohi.

Wasu 'yan takarar kan nuuna suna goyon baya ga wadannan kudurai masu farin jini a kudancin kasar nan da ma tsakiyar Najeriya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel