Dole ne mu ciyo bashi don ayyukan raya kasa da manyan ayyuka - Buhari

Dole ne mu ciyo bashi don ayyukan raya kasa da manyan ayyuka - Buhari

- Shugaba Buhari ya bayyana wa AFREXIM zaici gaba da neman taimakon su wajen gyara ga lalatattun kayayyakin kasar

- Karku gajiya damu saboda zamuyi ta zuwa, muna rokon ku daku yi mana sauki

- Mun Fahimci cewa muna bukatar kudin da zamu gyara titina, hanyoyin jirgin kasa, wuta da kuma hanyoyin sadarwa

Dole ne mu ciyo bashi don ayyukan raya kasa da manyan ayyuka - Buhari

Dole ne mu ciyo bashi don ayyukan raya kasa da manyan ayyuka - Buhari

A ranar Alhamis ne Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bayyana wa wasu mambobi AFREXIM cewa zaici gaba da neman taimakon su har zuwa sanda zai kawo karshen gyararrakin da zai gudanar a kasar.

Shugaban ya bayyana haka ne a yayin da bankin yakai masa ziyara a Abuja karkashin jagorancin Mr. Benedict Okey.

Jawabin na Buhari ta bakin Shehu Garba mataimaki na musamman a bangaren kafofin watsa labarai yace" muna godiya da irin taimakon da kuke bamu sannan zamuci gaba da zuwar muku har zuwa kawo karshen matsalolin mu".

"Mun Fahimci cewa muna bukatar kudin da zamu gyara titina, mu samar da hanyoyin jirgin kasa, wuta da kuma kafofin sadarwa, saboda haka karku gajiya damu saboda zamuci gaba da zuwar muku, muna rokon ku daku saukaka mana".

DUBA WANNAN: Masu sanya ido kan zabuka sun fara isowa kasar nan don shawagi

Shugaba Muhammad Buhari yace kasar tana fuskantar matsaloli na gyare gyare da wanda zamu nemi abokan ciniyya masu gwabi.

Shugaba kuma ciyaman na AFREXIM Dr Oramah ya bayyana jindadin su sannan da kuma goyan bayansu ga gwamnatin Nageriya wajen aiki da bankin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel