Oshiomhole ya bawa wasu ministoci biyu wa'adin sati guda ko su fuskanci fushin jam'iyya

Oshiomhole ya bawa wasu ministoci biyu wa'adin sati guda ko su fuskanci fushin jam'iyya

Shugaban APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole, ya bawa ministan kula da filayen jirgin sama na kasa, Hadi Sirika, da takwaransa na kwadago, Dakta Chris Ngige, wa'adin mako guda su rantsar da dukkan mambobin bod dake karkashin ma'aikatunsu ko su fuskanci fushin jam'iyya.

Oshiomhole ya bayyana hakan ne a cikin wata takarda da ya aike ga ministocin biyu ta hannun mai taimaka masa a bangaren yada labarai, Simon Ebegbulem, ranar 11 ga watan Yuli.

A cikin wasikar, Oshiomhole, ya bayyana rashin jin dadinsa bisa gazawar ministocin wajen kaddamar da mambobin bod din ba duk da umarnin da shugaba Buhari ya bayar na yin hakan ga dukkan ministoci yayin zaman majalisar zartarwa na kasa da ake duk Laraba ta kowanne mako.

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar sabon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya gargadi masu son yin takara da su sani cewar APC ba zata bawa kowa tikitin takara kyauta ba.

Oshiomhole ya bawa wasu ministoci biyu wa'adin sati guda ko su fuskanci fushin jam'iyya

Oshiomhole ya bawa wasu ministoci biyu wa'adin sati guda ko su fuskanci fushin jam'iyya

Oshiomhole ya yi wannan gargadi ne a yau, Alhamis, yayin rantsar da wani kwamiti na jam'iyyar APC a Abuja.

Kazalika ya bayyana cewar zasu dauki matakan ladabtarwa ga duk dan jam'iyyar da ya yi yunkurin yiwa kundin dokokinta zagon kasa.

DUBA WANNAN: An samu barkewar hargowa da yamutsi a zauren majalisa saboda ambaton R-APC

"Muna da hanyoyin fitar da 'yan takarar a APC, idan kana ganin zaka iya murda daliget yadda kaga dama, zamu iya bawa iya cewa 'yan jam'iyya ne zasu zabi dan takara, kamar yadda yake a cikin kundinmu," inji Oshiomhole.

Oshiomhole ya cigaba da cewa, "ba zamu saba doka domin farantawa wani ba. Babu abinda zai firgita mu ko ya bamu tsoro. Zamu bawa dukkan 'yan jam'iyya damar tsayawa zabe domin su bayar da gudunmawar su wajen gina Najeriya."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel