Ashe hana sayar da kodin kuma yana da tasa illar ga Najeriya

Ashe hana sayar da kodin kuma yana da tasa illar ga Najeriya

- Haramta amfani da sinadarin nan na Codeine a cikin maganin tari ka iya haifar da rashin aikin yi ga mutane 23,000

- A maimakon hakan za'a iya kayyade yanda za'a dinga amfani dashi

- A watan Mayun daya gabata ne gwamnatin tarayya ta bawa hukumar NAFDAC umarnin hana amfani da sinadarin na Codeine a cikin maganin

Ashe hana sayar da kodin kuma yana da tasa illar ga Najeriya
Ashe hana sayar da kodin kuma yana da tasa illar ga Najeriya

A ranar Alhamis ne ma'aikatan dake samar da sinadarai suka bayyana wa gwamnatin tarayya cewa Haramta amfani da sinadarin nan na Codeine a cikin maganin tari ka iya janyo rashin aikin yi ga mutane 23, 000.

Shugaban hukumar samar da sinadarai ta (NUCFRLAMPE) Mr Babatunde Olatunji shiya bayyana hakan a yayin da yake amsawa manema labarai tambayoyin su a Lagos.

Olatunji ya koka matuka inda ya shawarci gwamnatin tarayyar data kayyade yanda za'a dinga amfani da sinadarin a maimakon hana amfani dashi gaba daya don gujewa fadawa cikin rashin aikin yi.

DUBA WANNAN: Jonathan ya kaiwa Kayode ziyara

NAN ta bayyana mana cewa a watan Mayun daya gabata ne gwamnatin tarayyar ta bawa NAFDAC umarni data janye lamunin saka Codeine a cikin maganin tari.

Olatunji yace Haramta amfani da sinadarin na Codeine ka iya janyowa ma'aika 23,000 su rasa aikin su, yayin da kamfanoni da dama masu sarrafa maganin tari zasu rufe.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng