Ga abinda NYSC ta gano kan batun 'satiffiket na bogi' na Kemi Adeosun

Ga abinda NYSC ta gano kan batun 'satiffiket na bogi' na Kemi Adeosun

Hukumar NYSC ta sanar da yan Najeriya a ranar litinin cewa ministan kudi, Kemi Adeosun ta nemi shaidar fitarwa daga hukumar, hukumar a halin yanzu tana shirye shiryen wanke ministan daga zargin yin shaida ta bogi da ake mata,inji majiyar mu.

Majiyar tamu daga hukumar ta sanar damu cewa an tsaurara wa hukumar domin ta wanke Mrs Adeosun ta kowane hali.

"Daga cikin shirin, sun fara aiwatar da na farko, shine cewa ministan tana cikin jerin mutanen da suka nemi shaidar daga hukumar" inji majiyar mu.

"Yanzu abu na gaba shine zasu ce, bayan neman shaidar, hukumar ta bata amma wanda ya bada ne basu kai ga tantancewa ba.

"Amma tabbas ba laifin matar bane saboda tayi duk tsarin neman shaidar kuma an bata, don haka bata san ingantacciyar bace ko akasin hakan."

Yau fiye da kwana biyar kenan da muka ji cewa asirin ministan ya tonu sakamakon shaidar NYSC ta bogi da ta mallaka. Martanin hukumar ba magana mai tayi bace.

DUBA WANNAN: An janye 'yansanda daga gidan Fayose

A ranar litinin da yamma, hukumar ta maida martani tana cewa, Ministan ta nemi shaidar kuma zasuyi binciken inda ta samu shaidar da ake zargi.

Majiyar mu ta tabbatar mana da cewa hukumar bata ba Mrs Adeosun wata shaida ba saboda rahoto ya nuna cewa an dau lokaci ana duba rijistar hukumar ta mutanen da aka ba shaidar amma babu alamar sunan ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel