Dalilin da yasa na tsaya takarar shugabancin kasa - Atiku ya budewa 'yan majalisa cikinsa

Dalilin da yasa na tsaya takarar shugabancin kasa - Atiku ya budewa 'yan majalisa cikinsa

Atiku Abubakar, mai neman PDP ta tsayar da shi takarar shugabancin kasa ya gana da 'yan majalisar wakilai na jam'iyyar a daren ranar Talata.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar ta wakilai, Chukwuka Onyema, ne ya jagoranci tawagar 'yan majalisar.

Atiku ya yi amfani da damar da ya samu ta ganawa da 'yan majalisar wajen shaida masu dalilan da suka sa shi neman takarar shugabancin kasa.

Da hannunsa, Atiku, ya raba takardar niyyarsa ta yin takara ga 'yan majalisar ta PDP da kuma wasu na R-APC.

Dalilin da yasa na tsaya takarar shugabancin kasa - Atiku ya budewa 'yan majalisa cikinsa

Atiku Abubakar

A cikin takardar da ya raba, Atiku, ya sanar da 'yan majalisar cewar ya fito takarar ne domin kubutar da Najeriya da ceto ta da kuma gyara ta. Kazalika ya nuna kwarin gwuiwar cewar 'yan majalisar zasu goya masa baya.

A nasu bangaren, 'yan majalisar, ta bakin Onyema, sun tunawa Atiku muhimmancin samum tikitin takara kyauta ga 'yan majalisun.

DUBA WANNAN: An samu barkewar hargowa da yamutsi a zauren majalisa saboda ambaton R-APC

Atiku dai ya kafe kan cewar gwamnatin shugaba Buhari ta gaza ta kowacce fuska tare da bayyana cewar tun daga 1999 zuwa yanzu, ba a samu gwamnatin da ake tafka rashawa da cin hanci kamar gwamnatin APC ba.

Kazalika ya dauki alkawarin tona asirin duk cin hancin dake cikin gwamnatin ta APC da zarar ya zama shugaban kasar Najeriya, idan an zabe shi a 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel