Gwamna Tambuwal ya yi magana a kan harin Sokoto, ya bayyana adadin mutanen da aka kashe

Gwamna Tambuwal ya yi magana a kan harin Sokoto, ya bayyana adadin mutanen da aka kashe

Adadin mutanen da suka rasa rayukansu a hare-haren Sokoto ya cimma 39, kamar yadda gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal, ya fada a yau, Alhamis.

Tambuwal ya kara da cewar an gano karin wasu gawarwakin bayan 32 na farko da aka binne.

An Kai hari na baya-bayannan ne a karamar hukumar Rabah a jerin wasu hare-hare da aka jihar cikin 'yan kwanakinnan.

Da yake jawabi yayin karbar bakuncin wasu gwamnoni 5 da suka zo yi masa jaje, Tambuwal ya bayyana cewar wannan shine karo na farko da jama'a da rayukan jama'a da dama suka salwanta sakamakon wani hari.

Gwamna Tambuwal ya yi magana a kan harin Sokoto, ya bayyana adadin mutanen da aka kashe

Gwamna Tambuwal

"Yanzu haka akwai sansanin 'yan gudun hijira dake dauke da mutane fiye da 10,000 a yankin da abun ya shafa," in ji Tambuwal.

Tambuwal ya kara da cewar yamzu haka an aike da jami'an tsaro domin cigaba da sintiri a yankunan dake fama da hare-haren 'yan ta'adda.

Adamu Aliero, tsohon gwamnan jihar Kebbi kuma Sanata mai ci, ya dora alhakin kai harin a kan 'yan bindiga.

DUBA WANNAN: Da duminsa: ‘Yan Boko Haram 113 da matansu sun gamu da fushin kuliya, an yanke masu hukunci

Jagoran tawagar gwamnonin kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Abdulaziz Yari, ya bayyana cewar tilas shugabanni su hada kai domin kawo karshen asarar rayuka da dukiyoyi a sassan jihohin kasar nan.

Kazalika ya nuna damuwa bisa ga harin na jihar Sokoto tare da shaidawa Tambuwal din cewar irin wadannan hare-hare sun dade suna faruwa a jiharsa ta Zamfara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel