Ko APC ta yi adalci ko ta yi nadama – Nyako

Ko APC ta yi adalci ko ta yi nadama – Nyako

Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Murtala Nyako ya gargadi Jam’iyyar APC da ta yi adalci wajen tafiyar da lamuranta ko kuma abin da ya sami Jam’iyyar PDP ya shafe ta.

Nyako ya bayyana haka ne lokacin da yake yi wa mambobin Jam’iyyar APC da suka fito daga kananan hukumomii 21 na jihar, inda ya ce ya yi imani sabon shugaban Jam’iyyar APC ta kasa, Adams Oshiomhole zai iya gyara matsalolin da suka shafi jam’iyyar.

Ya ce har yau APC ba ta gane kurenta ba wajen daukar darasi daga abin da ya janyo koma baya ga Jam’iyyar PDP.

Tsohon Gwamnan ya nuna damuwa game da yadda Gwamnatin Jihar Adamawa ta mamaye harkokin jam’iyyar inda a cewarsa an sanya sunayen bogi cewa an yi zaben unguwanni alhalin a unguwa daya kawai aka yi zaben.

Ko APC ta yi adalci ko ta yi nadama – Nyako

Ko APC ta yi adalci ko ta yi nadama – Nyako

Ya ce an saba gudanar da zabe a yankinsa na Mayo Belwa tun 1957, amma abin takaici shi ne ganin yadda aka kawo wani cewa a zabe shi a dole wanda hakan bai taba faruwa ba.

Ya kara da cewa Jam’iyyar APC ta saki hanya mai kyau da ake tsammani ta kamanta adalci, ta bari wadansu tsirarin mutane na canja mata alkiblarta ta kamanta adalci.

KU KARANTA KUMA: Makiyayi ya kashe wani sufeton dan sanda a Kebbi

Ya ce idan ana son gwamnati ta yi mulki mai kyau sai an sanya matakan tsaro da hana fadace-fadace, domin rashin wadannan abubuwan na kawo koma bayan kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel