Bayan janyewar sojoji, 'yan bindiga sun cigaba da cin karensu babu babbaka a hanyar B/Gwari

Bayan janyewar sojoji, 'yan bindiga sun cigaba da cin karensu babu babbaka a hanyar B/Gwari

Bayan makonni hudu da matafiya su kayi cikin kwanciyar hankali, 'yan fashi da masu garkuwa da mutane sun sake kunno kai inda suka sace mutane da dama a daren Laraba da subahin Alhamis.

A yayin da yake hira da PRNigeria a wayar tarho, Awwali Nagote wani direba da ya tsira da kyar daga harin da yan bindigan suka kai, yace 'yan bindigan sace mutane da dama sun shiga dasu cikin daji.

Mr Nagote yace: "Na biyo hanyar kauyen Labi dake babban titin Birnin Gwari sai na hango motocci da dama mafi yawancinsu motoccin hana ne anyi parkin gefen titi yayin da su kuma yan bindigan ke tattara mutane zuwa cikin daji.

Bayan janyewar sojoji, 'yan bindiga sun cigaba da cin karensu babu babbaka a hanyar B/Gwari

Bayan janyewar sojoji, 'yan bindiga sun cigaba da cin karensu babu babbaka a hanyar B/Gwari

"Daga nan sai wasu daga cikin yan bindagan suka fara harbinmu, hakan yasa muka juya muka tsere.

"Daya daga cikin motoccin da aka kama motar Simintin BUA ce har ma da wasu manyan motoccin kamfanin Dangote da wasu treloli dake hanyarsu na zuwa Legas."

DUBA WANNAN: Majalisa ta fada cikin rudani bayan Sanatan APC ta zargi Majalisar da fifita Sanatocin PDP Read

An kuma ruwaito cewa jami'an tsaro da 'yan banga sun ceto wasu daga cikin wadanda yan bindigan suka sace.

Wani shugaban 'yan banga da ya bukaci a sakayya sunansa yace: "Masu garkuwa da mutanen su kirkiro sabuwar salo na tsayawa a wuraren da jami'an tsaro ke tsayawa idan sun kafa shinge sai dai sukan bari zai jami'an tsaron sun tashi daga aiki sannan sai su tsaya a wuraren suna tare mutane."

"Sun kashe wasu daga cikin mutanen da su kayi garkuwa dasu a jiya da safiyar yau a kusa da Labi dake titin Birnin Gwari.

Da aka tuntube shi, Kakakin hukumar Yan sanda na jihar Mr. Mukhtar Aliyu yace bai samu cikaken rahoton abinda a hanyar Birnin Gwarin ba amma yace hukumar ta kara adadin jami'an dake Sintiri a hanyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel