Ranar Arfa: Majalisar tarayya ta bukaci hukumar INEC ta canza ranakun zabukan fitar da gwani

Ranar Arfa: Majalisar tarayya ta bukaci hukumar INEC ta canza ranakun zabukan fitar da gwani

Majalisar wakilan Najeriya a ranar Laraba ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission, INEC da ta sake duba yiwuwar canza ranakun zabukan fitar da gwani na jam'iyyun kasar.

Wannan kiran dai kamar yadda Honorable Balarabe Salame daga jihar Sokoto ya gabatar da kudurin, ya ce ya zama dole ne musamman idan akayi la'akari da yadda ranakun suka zo kwana biyu kacal kafin ranar Arfa.

Ranar Arfa: Majalisar tarayya ta bukaci hukumar INEC ta canza ranakun zabukan fitar da gwani

Ranar Arfa: Majalisar tarayya ta bukaci hukumar INEC ta canza ranakun zabukan fitar da gwani

KU KARANTA: Kotu ta kwace kadarorin wani gwamna a Arewa

Legit.ng ta samu cewa dan majalisar ya kara da cewa ranar 18 ga watan Agusta mai zuwa ce ranar da aka sanya za'a yi zabukan fitar da gwamni amma kuma ranakun 20 da 21 ne ake sa ran yin Arfa.

Wannan dai kamar yadda yace zai takurawa musulmai da dama musamman ma ganin irin fa'idar da ranar ke da ita a addinin musulunci kuma kasantuwar wasu ma sukan je Saudiyya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel