Yanzu-Yanzu: Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kwashe dukkan jami'an tsaron gidan gwamnatin jihar Ekiti

Yanzu-Yanzu: Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kwashe dukkan jami'an tsaron gidan gwamnatin jihar Ekiti

Labarin da muke samu da dumin sa daga majiyar mu ta Sahara Reporters, yanzu na cewa ne rundunar 'yan sandan Najeriya sun bayar da umurnin kwashe dukkan jami'an ta daga gidan gwamnatin jihar Ekiti.

Wannan umurnin dai kamar yadda majiyar ta mu ta bayyana yana kunshe ne a cikin wata takarda da hedikwatar 'yan sandan ta kasa ta aike zuwa gidan gwamnatin a yau dinnan.

Yanzu-Yanzu: Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kwashe dukkan jami'an tsaron gidan gwamnatin jihar Ekiti

Yanzu-Yanzu: Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kwashe dukkan jami'an tsaron gidan gwamnatin jihar Ekiti

KU KARANTA: Rashawa: Atiku yayiwa Buhari wankin babban bargo

Legit.ng ta samu cewa sai da a cikin takardar, an ce dogaran gwamnan biyu da shugaban masu bayar da tsaron gidan gwamnatin da kuma wasu jami'ai biyar ne kawai aka lamuncemawa su zauna.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a jiya ma dai anyi gumurzu a gaban gidan gwamnatin jihar inda har ma gwamnan, Ayodele Fayose yace wani dan sanda ya mare shi sannan kuma an watsa masa barkonon tsohuwa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel