2019: PDP za ta takaita yawan masu neman takarar Shugaban kasa

2019: PDP za ta takaita yawan masu neman takarar Shugaban kasa

Babbar Jam’iyyar Adawa ta PDP za ta takaita yawan masu son tsayawa takarar neman kujerar Shugaban kasa a zaben 2019 da ke tafe, domin kauce wa rudani a daidai lokacin da zaben fid-da- gwani ke karatowa.

Wadansu kososhin Jam’iyyar PDP sun bayyana wa Aminiya cewa a yanzu haka jam’iyyar tana da yawan masu son tsayawa takara da suka nuna sha’awar neman kujerar shugabancin kasa.

Masu neman takara karkasahin lemar PDP sun hada da tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi.

2019: PDP za ta takaita yawan masu neman takarar Shugaban kasa

2019: PDP za ta takaita yawan masu neman takarar Shugaban kasa

Haka zalika akwai tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido na cikin masu hararar kujerar da sauran wasu jiga-jigan jam'iyyar.

KU KATARANTA KUMA: Cikakken jawabin shugaba Buhari a wajen kaddamar da tashan jirgin kasan Abuja

Hasashe na nuna cewa idan har suka rage yawan masu takara hakan zai fi yin tasirin yadda za su karbe mulki daga hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa.

An tattaro cewa akwai yiwuwar shigowar karin wadansu ’yan takara daga jam’iyyu da daban-daban da za su sauya sheka zuwa PDP musamman daga APC, wadanda suka ce hakan zai haifar da cincirindo muddin ba a dauki wani mataki da wuri ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel