Na hannun daman Shugaban kasa Buhari da ake zargi da cin amana

Na hannun daman Shugaban kasa Buhari da ake zargi da cin amana

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hau mulki ne dai a 2015 bayan ya doke Shugaban Kasa Goodluck Jonathan. Daga cikin abin da ya sa Buhari yayi nasara a zaben shi ne irin rikon sa da gaskiya da rikon amana.

Sai dai kuma kawo yanzu ana zargin wasu Mukarabban Shugaban kasar da laifi na rashin gaskiya ko cin amana ko satar dukiyar al’umma. Daga cikin wadanda ake zargi da wannan laifi a Gwamnatin Buhari akwai:

Na hannun daman Shugaban kasa Buhari da ake zargi da cin amana

Ana zargin irin su Abba Kyari da laifin karbar cin hanci

1. Kemi Adeosun

Ana zargin Ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun da laifin amfani da jabun takardar shaida na NYSC ban da kuma laifin da tayi na kin yi wa kasa hidima. Jiya wani tsohon Jami’in Hukumar bauta na kasa watau NYSC ya tabbatar mana da cewa satifiket din bogi ne a hannun Ministar.

KU KARANTA: Kemi Adeosun: Gwamnatin Najeriya tayi magana

2. Obono Obla Okoi

Kwanaki dai Hukumar Jarrabawar nan ta WAEC ta tabbatar da cewa sakamakon jarrabawar Okoi Obono-Obla wanda yana cikin masu ba Shugaban kasa Buhari shawara ba na gaskiya bane. Wani babban Jami’in na WAEC Femi Ola ya tabbatar da wannan a gaban Majalisar Kasar.

3. Abba Kyari

Ana zargin cewa Kamfanin sadarwa na MTN ta ba Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban kasa cin hancin kudi har Naira Miliyan 500. Ana zargin MTN ta ba Abba Kyari wannan kudi ne lokacin da aka ci ta tara domin a rage adadin tarar. MTN dai ta karyata wannan amma ta kori Ma’aikatan ta.

4. Tukur Buratai

Shugaban Hafsun Sojan Najeriya Laftana Janar Tukur Buratai ya ga ta kan sa kwanaki lokacin da aka huro masa wuta na mallakar wasu manyan gidaje a Birnin Dubai da ke kasar Larabawa. Janar Buratai dai yace Iyalan sa ne su ka saye gidan da kyar kuma tun kafin ya zama Hafsun Soji.

5. Abdurrasheed Maina

Gwamnatin Buhari ce tayi kutun-kutun ta dawo da Abdurrasheed Maina bakin aiki bayan zargin yin sama da fadi da Naira Biliyan 100 na kudin fansho. Ministan shari’a Abubakar Malami ne yayi wannan danyen aiki kuma ya hana Majalisr Dattawan Kasar da Kotu yin bincike game da lamarin.

Kafin nan dai Shugaban kasa Buhari ya sallami Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir David Lawal da kuma wasu a Gwamnatin sa bayan an kama su da laifin aikata ba dai-dai ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel