2019: Babu ragowar tikitin takara kyauta a APC, tilas sai an yi gumurzu - Oshiomhole

2019: Babu ragowar tikitin takara kyauta a APC, tilas sai an yi gumurzu - Oshiomhole

Sabon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya gargadi masu son yin takara da su sani cewar APC ba zata bawa kowa tikitin takara kyauta ba.

Oshiomhole ya yi wannan gargadi ne a yau, Alhamis, yayin rantsar da wani kwamiti na jam'iyyar APC a Abuja.

Kazalika ya bayyana cewar zasu dauki matakan ladabtarwa ga duk dan jam'iyyar da ya yi yunkurin yiwa kundin dokokinta zagon kasa.

2019: Babu ragowar tikitin takara kyauta a APC, tilas sai an yi gumurzu - Oshiomhole

2019: Babu ragowar tikitin takara kyauta a APC, tilas sai an yi gumurzu - Oshiomhole

DUBA WANNAN: Sai an kori bara-gulbi daga cikin jami'an soji sannan za a iya shawo kan kashe-kashe a Najeriya

"Muna da hanyoyin fitar da 'yan takarar a APC, idan kana ganin zaka iya murda daliget yadda kaga dama, zamu iya bawa iya cewa 'yan jam'iyya ne zasu zabi dan takara, kamar yadda yake a cikin kundinmu," inji Oshiomhole.

Oshiomhole ya cigaba da cewa, "ba zamu saba doka domin farantawa wani ba. Babu abinda zai firgita mu ko ya bamu tsoro. Zamu bawa dukkan 'yan jam'iyya damar tsayawa zabe domin su bayar da gudunmawar su wajen gina Najeriya."

Tsohon gwamnan jihar Edo ya kara da cewa lokacin nada 'yan jam'iyyar adawa a mukaman gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Buhari ya kare.

"Muna sane da cewar har yanzu akwai 'yan jam'iyyar PDP da yawa dake rike da mukaman siyasa a hukumomin gwamnatin tarayya. Zamu yi duk mai yiwuwa domin zazzage duk wani dan PDP dake cigaba da rikon wata ma'aikata ko hukumar gwamnatin tarayya," a cewar Oshiomhole.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel