Babban dan siyasa a arewa ya bawa Buhari kyautar motocin kamfen 13 da katafaren Ofis

Babban dan siyasa a arewa ya bawa Buhari kyautar motocin kamfen 13 da katafaren Ofis

A yayin da shekarar 2019 ke kara matsowa kuma al'amuran siyasa ke kara daukan zafi, daya daga cikin 'yan takarar kujerar gwamnan jihar Gombe a jam'iyyar APC, Alh Farouk Bamusa, ya bayar da kyautar motoci 13 da katafaren Ofis domin yiwa Buhari yakin neman zabe.

Da yake magana da manema labarai, jim kadan bayan mika kyautar motocin da ofishin ga jam'iyyar APC ta jihar Gombe, Bamusa, ya bayyana cewar dole duk wani dan Najeriya mai akidar son cigaba ya bayar da gudunmawar sa domin samun nasarar shugaba Buhari a zaben 2019.

Babban dan siyasa a arewa ya bawa Buhari kyautar motocin kamfen 13 da katafaren Ofis

Babban dan siyasa a arewa ya bawa Buhari kyautar motocin kamfen 13 da katafaren Ofis

DUBA WANNAN: Ina zawarawa da 'yan mata, Dangote yace yana bukatar sake kara mata

Bamusa ya bayyana cewar 'yan Najeriya sun ga gagarumin canji a kowanne bangare na cigaban kasa a karkashin jagorancin shugaba Buhari. Sannan ya kara da cewa, Buhari ya cancanci samun wata damar domin samun cigaba da aiyukan da ya fara.

Ya ambaci yaki da cin hanci da aiyukan ta'addanci da inganta tattalin arziki a matsayin wasu daga cikin nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu.

Da yake magana a kan burinsa na zama gwamna, Bamusa, ya bayyana cewar burinsa shine ceto jihar Gombe daga mulkin kama-karya dake barazanar durkushewar harkokin gwamnati a jihar.

"Gwamnatin PDP ta bata komai a jihar Gombe. Babu tayi yawa; babu ruwan sha, harkar lafiya ta lalace, matasa ba aikin yi. Zan zo da sabon tunani domin kawowa mutane cigaba, a cewar Bamusa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel