Babbar magana: Jerry Gana ya kaddamar da takararan shugaban kasa a SDP

Babbar magana: Jerry Gana ya kaddamar da takararan shugaban kasa a SDP

Tsohon ministan sadarwa na Najeriya, Farfesa Jerry Ghana ya sanar da cewa zai tsaya takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar SDP a zaben 2019 mai zuwa kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Jerrry Ghana ya ce gwamnati mai ci a yanzu ta nuna gazawarta a bangarori da yawa na mulki hakan yasa yake ganin bai dace jam'iyyar APC ta sake zarcewa ba.

Tsohon ministan yace a halin yanzu Najeriya na ciki tsaka mai wuya kuma idan ba'a dauki mataki ba rikicin da zai barke a kasar sai ya fi wanda akayi a yakin Biafra.

Babbar magana: Jerry Ghana ya kaddamar da takararan shugaban kasa a SDP

Babbar magana: Jerry Ghana ya kaddamar da takararan shugaban kasa a SDP
Source: Depositphotos

A bangarensa, mataimakin shugaban jam'iyyar SDP, Dr Ishaq Abdul Ahmed wanda ya samu wakilcin ciyanman din jam'iyyar na kasa Olu Falae yace Jerry Ghana mutum ne mai daraja da nagarta a Najeriya da jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel