Bugaggen dan sandan Najeriya ya bindige wata mata

Bugaggen dan sandan Najeriya ya bindige wata mata

Mutanen birnin Calabar na jihar Kuros Riba sun shiga cikin halin juyayin mutuwar wata mata, Victoria Epe, da wani saja a hukumar 'yan sanda mai suna Nkanu ya harbe.

Lamarin ya faru ne cikin kasa da sati biyu bayan wani dan sanda ya harbe wata budurwa dake bautar kasa a Abuja.

Jaridar Leadership ta rawaito cewar dan sandan ya harbi matar ne a unguwar Ikot Ansa dake karamar hukumar birnin Calabar.

Bugaggen dan sandan Najeriya ya bindige wata mata

Bugaggen dan sandan Najeriya ya bindige wata mata

DUBA WANNAN: Mutum uku ne ashe suka kashe diyar mataimakin gwamnan Ondo

Wakilin jaridar ta Leadership da ya ziyarci gidan su marigayiyar mai lamba 11 dake kan titin Joseph Mkpa a unguwar Ikot Ansa, ya samu 'yan uwa da Makwabtan marigayiyar cikin juyayi da alhini.

Daya daga cikin 'yan uwan marigayiya Victoria ta bayyana cewar 'yar uwar ta su ba mai son fitina ba ce tare da bayyana mamakin yadda dan sandan ya kashe masu 'yar uwa.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewar dan sandan, dan asalin karamar hukumar Abi ta jihar Kuros Riba, ya harbe Victoria ne bayan ya dawo a buge daga wurin wani biki da misalin 8:30 na dare.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel