Majalisa ta fada cikin rudani bayan Sanatan APC ta zargi Majalisar da fifita Sanatocin PDP

Majalisa ta fada cikin rudani bayan Sanatan APC ta zargi Majalisar da fifita Sanatocin PDP

An shiga rudani a majalisar dattawa a yau Laraba 11 ga watan Yuli bayan Sanata Remi Tinubu mai wakiltar yankin Legas ta tsakiya tayi korafi kan rashin adalci da tace Sanatocin PDP na yiwa Sanatocin APC a majalisar.

Tinubu ta koka da cewa a matsayinta na Sanata mai mukami kuma yar jam'iyyar dake da rinjaye a majalisar, itace ya dace a bata damar gabatar da kudiri ba wai wani Sanata daga jam'iyyar mara rinjaye ba kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Hakan ya faru ne bayan mataimakain shugaban majalisar, Sanata Ike Ekweremadu ya bukaci Sanata Gilbert Nnaji na jam'iyyar PDP ya gabatar da kudirin bitar fara karanto abubuwan da majalisar ta tattauna a jiya kafin a dora da na yau.

Sanatar APC tayi korafi kan banbanci da ake nuna musu a majalisar dattawa

Sanatar APC tayi korafi kan banbanci da ake nuna musu a majalisar dattawa

DUBA WANNAN: Ina zawarawa da 'yan mata, Dangote yace yana bukatar sake kara mata

Bayan Sanata Nnaji ya gabatar da kudirin ne sai Sanata Remi Tinubu tayi zumbur ta mike ta bayyana rashin amincewarta kan yadda shugaban majalisar ke fifita sanatocin jam'iyyu marasa rinjaye.

Wannan kalaman na Remi Tinubu ya sanya majalisar ta rikice inda sauran Sanatocin PDP suka bayyana rashin amincewarsu da kalaman data furta.

Kalamanta: "Mune keda rinjaye a majalisar, ya kamata a zabi masu rinjaye kafin marasa rinjaye kuma duk da cewa ina girmama ka, ya kamata ka sani cewa na riga ka zuwa wannan majalisar."

Sai dai daga baya, Sanata Remi Tinubu ta amince ta goyi bayan kudirin don a fara tattauna kudirorin dake gaban majalisar amma tace tayi hakan ne saboda kada a bata lokaci kuma sanatan da ya gabatar da kudirin shima ba sabon shiga bane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel