Kuma dai! Hukumar kwastam ta damke kwantena dauke da muggan makamai

Kuma dai! Hukumar kwastam ta damke kwantena dauke da muggan makamai

Hukumar kwastam na Najeriya shiyar tashar jirgin Tin Can da ke Legas, ta damke kwantena dauke da manyan makami a ranan Litinin da Talata, 10 da 11 ga watan Yuli, 2018.

Kwantrolan hukumar na shiyar Tin Can, Musa Abdullahi, ya bayyana hakana Legas cewa an gano harsasai 150 a Terminal ‘C’ sannan aka damke wukake 28 cikin wani kwantena mai lamba TGHU 60143419.

Yace: “Na bada umurnin tura wannan kwantena mai lamba TGHU 60143419. Sashen ladabtarwa inda aka gudanar da bincike aka gano harsasai 150 da kuma wukake 28.”

“Wadannan abubuwa sun sabawa dokokin hukumar. Amma a yanzu mun damke wanda ke dauke da motan kuma yana bangaren binciken jam’iyyar.”

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya kaddamar da tashan jirgin kasan birnin tarayya Abuja

Abdullahi ya kara da cewa ranan Talata cewa an damke wani mota dauke da jaka kunshe da wasu harsasai.

Kwantrolan ya ce an gano harsasai 149 na 38MM, harsasai 92 na 9MM da kuma carbin harsasai 11.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel