Zamu tabbatar da cewa an kori dukkan yan jam’iyyar PDP a ma’aikatun gwamnati – Shugaban APC, Oshiomole

Zamu tabbatar da cewa an kori dukkan yan jam’iyyar PDP a ma’aikatun gwamnati – Shugaban APC, Oshiomole

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta shirya tsaf domin cire dukkan mambobin jam’iyyar adawa, Peoples Democratic Party (PDP), masu rike da kujeru a ma’aikatun gwamnatin tarayya.

Jam’iyyar ta lashi takobin cewa za ta an aiwatar da manufar canji na tabbatar da cewa babu dan adawan da zai yi aiki a ma’aikatar gwamnati saboda ba manufarsu daya ba.

Shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole, a jiya Talata, 11 ga watan Yuli ya bayyana hakan ne yayinda yake rantsar da sabbin shugabannin jam’iyyar a sakatariyar jam’iyyar da ke birnin tarayya a Abuja,

Oshiomhole ya jaddada cewa jam’iyyar shirya take da tattaunawa da mambobin jam’iyyar na gaske masu ganin cewa ana cin zarafinsu, amma fa ba za’a bari wasu yan cirani su mamaye jam’iyyar ba.

KU KARANTA: Ku kara hakuri hukumomin tsaro na suna aiki tukuru – in ji Buhari

Oshiomole yace: “A yau, muna da mambobin jam’iyyar PDP da dama suna rike da manyan kujeru a ma’aikatun gwamnatin tarayya. Za mu yi dukkan mai yiwuwa domin tsige wadannan mutanen daga kujerunsu saboda mu jam’iyyar canji ne. Su yan jam’iyyun gargajiya ne kuma ba zamu iya barin yan gargajiya su samar da canjinmu ba.”

“Saboda haka, hakki ne akanmu na gamsar da fadar shugaban kasa cewa babu ruwan wannan gwamnati da duk wani dan jam’iyyar PDP da ke rike da babban kujera a ma’aikatun gwamnati .”

Zamu tabbatar da cewa an kori dukkan yan jam’iyyar PDP a ma’aikatun gwamnati – Shugaban APC, Oshiomole

Zamu tabbatar da cewa an kori dukkan yan jam’iyyar PDP a ma’aikatun gwamnati – Shugaban APC, Oshiomole

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Shugaban jamiyyar APC Adams Oshiomhole ya bayyana cewa dukkanin masu shirin barin jamiyyar na a matsayin 'yan cirani ne, kuma marasa akidar taimakon al'umma sai bukatar kansu.

Ya kara da cewa duk wadanda suke da tabbataccen korafi to babu shakka ba za su taba ficewa daga Jamiyyar ta APC ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel