Bana yin nadamar safarar Alburusai 20,000 zuwa Najeriya – wanda ake zargi

Bana yin nadamar safarar Alburusai 20,000 zuwa Najeriya – wanda ake zargi

- Kwastam ta yi babban kamu a arewacin Najeriya

- Yanzu haka dai wasu mutane da suka shigo da harsahi mai yawan gaske su shiga hannu

- Amma abin mamaki shi ne daya daga cikin wadanda ake zargin ya ce ba ya nadama

Hukumar hana fasa kwauri ta kasa ta samu nasarar cafke wasu mutane biyu da suka yo safarar alburushin bindiga da yawansa ya kai 200,000, yayin da suke kokarin shigow da shi ta kan iyakar kasar ta Wawa-Babana a Jihar Neja.

Bana yin nadamar safarar Alburusai 20,000 zuwa Najeriya – wanda ake zargi

Bana yin nadamar safarar Alburusai 20,000 zuwa Najeriya – wanda ake zargi

Jami’an hukumar masu kula da ofishin shiyar da ya hada da jahohin, Neja, Kwara da Kogi ne suka yi gagarumin kamun.

Hukumar Kwastam din ta bayyana sunayen mutanan da ake zargin da; Martin Anokwara da kuma wani mai suna Bukari Dauda.

Jaridar Leadership ta rawaito cewa wadanda ake tuhumar sun taso ne daga jamhuriyan Benin cikin babbar mota da ke makare da kwanson albarusai har 200,000 yayin da suka nufi zuwa garin Onitsha, ta Jihar Anambra dake kudancin Najeriya.

Guda daga cikin wadanda ake tuhumar mai suna Mista Anokwara, ya shaidawa ‘yan jaridu cewa, yayi balaguro ne zuwa kasar jamhuriyar Benin domin sayo albarusan don yake siyarwa ga mafarauta da kuma masu bindigogin da ke da lasisin hukuma a shiyyar kudu maso gabashin kasarnan.

KU KARANTA: Zaben jihar Ekiti: ‘Yan sanda sun kama wasu ‘yan PDP da dangwalallun kuri’un zabe

“Rayuwa ai kalubale ce gaba dayanta, ba zan ce na yi nadamar aikata hakan ba, saboda ina sane da abinda nake yi ba kuskure ne ba. Koma dai menene, a bari doka ta yi aikinta,” in ji Anokwara.

Shi ma direban motar mai suna Dauda, ya shaida wa manema labarai cewa, shi bai san abin da ke cikin motar ba, aikinsa kawai an dauke shi haya ya tuko motar ne kawai daga Kwatano zuwa Onitsha.

Kwamandan Kwastam na shiyyar, Benjamin Binga, cewa yayi, jami’ansu ne suka kama motar wacce ta shigo cikin kasarnan ta kan iyakan Babana da misalin karfe 3 daren ranar Litinin.

Benjamin Binga ya kara da cewa, babbar motar ta yi badda kama ne da jarkokin da babu komai a cikinsu sama da 100, amma da aka bincika sai aka gano akwai wata barauniyar ma’ajiya a kasan motar inda aka boye albarusan a ciki.

Bana yin nadamar safarar Alburusai 20,000 zuwa Najeriya – wanda ake zargi

Bana yin nadamar safarar Alburusai 20,000 zuwa Najeriya – wanda ake zargi

“Ba wani bayani aka ba mu a kan motar ba, mutane na ne suka yi aikinsu a cikin natsuwa, har sai da suka gano wannan almundahanar da aka shirya a kasar motar".

Sannan ya bayyana cewa “Albarusan dubbai ne, za mu shafe awanni don kirga su. A yanzun dai muna kokarin gano ainihin abinda ake son yi da albarusan, da kuma wanda ya turo a kawo su cikin kasarnan,” Binga ya shaida.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel