Ekiti: PDP za ta yi zanga-zangan lumana na gama gari

Ekiti: PDP za ta yi zanga-zangan lumana na gama gari

Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya umurci jami’an jam’iyyar na jihohi, shugabanni da masu ruwa da tsaki da su yi zanga-zangan lumana a hukumomin yan sanda dake dukkanin jihohin tarayya.

A cewar jam’iyyar za’a gudanar da zanga-zangan lumanan ne domin kakkabe abun da suka ambata da “cin zarafin yan sanda" a jihar Ekiti a ranar Laraba, wanda ya kai ga har yan sanda sun tozarta Gwamna Ayo Fayose.

Ekiti: PDP za ta yi zanga-zangan lumana na gama gari

Ekiti: PDP za ta yi zanga-zangan lumana na gama gari

A wata sanarwa daga sakataren shirye-shirye na jam’iyyar, Kanal Austin Akobundu (mai ritaya) a jiya, jam’iyyar ta bukaci dukannin reshen tan a jihohi da su gabatar da wasikar zanga-zanga ga sufeto janar na yan sanda, Ibrahim Idris ta hanyar kwamishinonin yan sandansu.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin APC na tsorata alkalai gabannin zabe - Obasanjo

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Kayode Fayemi, dan takarar gwamna karkashin jam’iyyar APC a zaben Ekiti da za’a yi a ranar, Asabar ya ce yana so ya sake mulkar jihar ne domin rage talauci a tsakanin mutane.

Ya bayyana hakan ne a gangamin karshe da APC ta yi gabannin zaben a filin wasa na Oluyemi Kayode dake Ado Ekiti a ranar Talata, 10 ga watan Yuli.

Mista Fayemi wadda ya yi gwamnan jihar daga 2010 zuwa 2014, ya bayyanawa taron jama’a cewa magajinsa, Gwamna Ayodele Fayose, ya muzgunawa jama’ar jihar ta hanyar kin biyan albashi da fansho.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel