Gwamnatin APC na tsorata alkalai gabannin zabe - Obasanjo

Gwamnatin APC na tsorata alkalai gabannin zabe - Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, cif Olusegun Obasanjo ya zargi gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsorata alkalai don taimakawa jam’iyyar APC, akan al’amuran zabe.

Obasanjo, wanda ya kasance dan adawan Buhari na wassu lokaci, yayi zargin cewa ana amfani da hukumomin dake yaki da cin hanci wajen kau da jam’yyun adawa.

Ya fadi hakane a Abuja a wani taron murnar cikar shekara 70 da haihuwar tsohuwar ministan harkokin mata da cigaba, Misis Josephine Anenih.

Gwamnatin APC na tsorata alkalai gabannin zabe - Obasanjo

Gwamnatin APC na tsorata alkalai gabannin zabe - Obasanjo

Ko da yake, tsohon shugaban kasan bai bayyana wadanda ake danne wa hakki ba, ya cigaba da cewa damokardiyya ta ba jam’iyyun adawa damar a saurareta kamar yanda ya kasance a tsarin gwamnatin jama’a, na jama’a, don jama’a.

KU KARANTA KUMA: Kiristocin Arewacin Najeriya sun yi wa Kabiru Turaki mubaya’a

Dangane da kasancewar mata a gwamnati, Obasanjo yace gwamnatin Buhari bata kai mataki na 35 ba ko.

Ya kuma yi kira ga a gyara kundin tsarin mulkin 1999 domin ba mata kaso 40 cikin dari a gwamnati.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta ruwaito cewa manyan Malaman addinin Kirista da ke Arewacin Najeriya da ke da jama’a har a irin su Kasar Amurka da Taiwan sun nuna cewa za su marawa tsohon Minista Kabiru Tanimu Turaki bayan zama Shugaban kasa a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel