Satifiket din bogi ne a hannun Kemi Adeosun inji tsohon Darektan NYSC

Satifiket din bogi ne a hannun Kemi Adeosun inji tsohon Darektan NYSC

Mun samu labari cewa wani tsohon Jami’in Hukumar bauta na kasa watau NYSC Anthony Ani ya tabbatar mana da cewa satifiket din bogi ne a hannun Ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun.

Satifiket din bogi ne a hannun Kemi Adeosun inji tsohon Darektan NYSC

An tona asirin Ministar Buhari da ake zargi da takardun bogi

Anthony Ani wanda tsohon Jami’in NYSC ne ya bayyana cewa akwai gaskiya a binciken da ‘Yan jarida su kayi game da satifiket din Ministar kudi ta Kasar. Ani ya bayyana wannan ne a gaban Duniya lokacin da yake magana a gidan Talabiji.

Gidan Talabijin na Channels TV tayi hira da Anothony Ani wanda ya tabbatar da cewa babu yadda za ayi Janar Yusuf Bomoi ya sa hannu a takardar shaidar Ministar domin kuwa a lokacin ya bar mtasayin sa na Shugaban Hukumar NYSC na kasar.

Anthony Ani wanda Darektan Hukumar ne na bangaren raba masu bautar kasan zuwa Jihohi da dama yace lokacin da ya kamata ace an ba Kemi Adoesun satifket din ta a karshen shekarar 2009, Janar Mahrazu Tsiga ne Shugaban NYSC.

KU KARANTA: An samu sabanin da ya so ya tada rikici a Majalisa

Tsohon Darektan dai ya tabbatar da cewa takardun Ministar na bogi ne kuma babu yadda za ayi ace ba tayi wa kasa bauta ba ganin cewa ta kammala Jami’a ne tana Budurwa. Ani yace har ‘Dan shekara 60 ya kan yi bautar kasa a Najeriya.

Ministan wasanni da na Matasa na kasar watau Solomon Dalung dai ya nemi Shugaban NYSC na yanzu Janar Suleiman Kazaure ya zo yayi masa bayanin abin da ke faruwa game da lamarin. Dalung yace da an gama bincike zai yi jawabi.

Kun san cewa Ministar kudin ta Najeriya Kemi Adeosun ba ta ce komai ba har yanzu bayan an dauki fiye da kwanaki 4 da aka zarge ta da amfani da shaidar bogi. Ana zargin cewa Ministar na amfani ne da takardar bautar kasa NYSC na jabu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel