Ana ta ce-ce-ku-ce game da abin da ya auku ga Gwamnan Ekiti Fayose

Ana ta ce-ce-ku-ce game da abin da ya auku ga Gwamnan Ekiti Fayose

Mun lura cewa abin da ake zargi ya auku ga Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose ya jawo ta-cewa a kasar nan. An dai ga Gwamnan yana ta shara kuka bayan yace an yi masa illa a wuyan sa bayan ‘Yan Sanda sun yi masa duka a gidan Gwamnati.

Ana ta ce-ce-ku-ce game da abin da ya auku ga Gwamnan Ekiti Fayose

Gwamna Ayo Fayose ya saba sukar Gwamnatin Buhari

Gwamna Ayo Fayose yayi ikirarin cewa Jami’an ‘Yan Sanda sun watsa masa borkonon tsohuwa a gidan Gwamnati sannan su ka rika fisgar sa a kasa don haka ya nemi a damke Sufata Janar din ‘Yan Sanda idan har wani abu ya faru a gare sa.

Sai dai jama’a sun ce akwai alamar tambaya a lamarin don kuwa Gwamna Fayose kadai ne yayi kukan cewa an watsa masa borkonon tsohuwar kuma babu yadda za ayi Jami’an tsaron sa su zauna hakan na faruwa gare sa ba su yi wani abu ba.

KU KARANTA: Buga Galadima na neman jawowa APC danyen aiki

A lokacin mulkin Goodluck Jonathan a zaben 2014, haka Gwamna Fayose ya ci karen sa babbaka inda ake zargin an yi amfani da karfin Soja wajen ba Ayo Fayose nasara. Yanzu dai wasu na ganin dara ce ta ci gida saboda irin sukar Buhari da yake yi.

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ta shafin sa na Tuwita yayi tir da abin da ya farun jiya a gidan Gwamnatin Jihar Ekiti. Atiku da sauran Jama’a dai sun nemi a rika buga siyasa da tsabta ba da gabar hauka ba kamar yadda ake gani.

A shekaran jiya ne dai Shugaban kasa Buhari ya shiga Jihar Ekiti inda ya tabbatar da cewa kamfe ya zo yi ba ramuwar gayya ba. Bayan nan ne dai wannan abu ya faru a gidan Gwamnatin Jihar Ekitin inda Fayose ke shirin barin kujerar sa ta Gwamna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel