Juma’ar da za tayi kyau: Atiku ya lashe zaben somin-tabi na Shugaban kasa

Juma’ar da za tayi kyau: Atiku ya lashe zaben somin-tabi na Shugaban kasa

A shekaran jiya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha kashi a wani zaben gwaji da aka yi a kafar sada zumunta na zamani na Tuwita. Shugaba Buhari ya sha kashi ne hannun Atiku Abubakar na babban Jam'iyyar adawa na PDP.

Juma’ar da za tayi kyau: Atiku ya lashe zaben somin-tabi na Shugaban kasa

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku na iya doke Buhari a 2019

An yi wani zabe domin a gane inda 2019 ta sa kai tsakanin Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da Shugaban kasa Buhari da kuma Gwamnonin Sokoto da na Jihar Gombe Aminu Waziri Tambuwal da Ibrahim Dankwambo.

A wannan zaben da aka yi, kashi 41% ne su ka nuna cewa idan har aka zo zaben 2019, za su zabi Atiku Abubakar. Kashi 31% ne kuma su kace su na tare da Shugaban kasa Buhari. Sai kuma kashi 17% su kace Dankwambo ne gwanin na su.

KU KARANTA: An nemi INEC ta sake duban jadawalin zaben 2019

Ragowar kashi 8% din kuma sun ce za su zabi tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Aminu Waziri Tambuwal ne a zaben na 2019. Sanata Ben Murray-Bruce da ke wakiltar Yankin Jihar Bayelsa karkashin Jam’iyyar PDP ne yayi wannan tinke.

Kwanakin baya kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust, YNaija tayi shigen irin wannan zabe inda Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya ba Shugaban kasa Buhari ‘dan karen kashi da kashi 70% da 19%.

A jiya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga Jihar Ekiti domin yi wa ‘Dan takarar APC kamfe. Kun ji cewa Shugaba Buhari da APC sun tara jama’a a Ekitin duk da ‘danyen shirin da Fayose ya shirya na hana jama’a zirga-zirga a cikin Jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel