Dalilai na na rabar da kudaden da aka karbo na Abacha ga talakawa - Buhari

Dalilai na na rabar da kudaden da aka karbo na Abacha ga talakawa - Buhari

- Abacha ya danqare biliyoyin daloli a Turai

- Ance wai tanadi yake wa Najeriya a lokacin

- Wasu sunce sacewa yayi domin ya ci shi kadai

Dalilina na rabar da kudaden da aka karbo na Abacha ga talakawa

Dalilina na rabar da kudaden da aka karbo na Abacha ga talakawa

Bayan da aka sake aikowa da Najeriya wasu kashi na biliyoyin Nairori zuwa ga gwamnati, da kuma shawarar gwamnati na raba su ga jama'a don suji kuma su gani a kasa, a karon farko shugaba Buhari yai bayanain dalilansa na rabar da kudin.

$322m ce dai wannan karon kasar Switzerland ta dawowa da Najeriya, cikin irin kudaden da Abachan ya boye a kasar shekaru 20 dadoriya da suka wuce.

A cewar shugaba Buhari, bakin talauci da jama'a ke fama dashi yasa yayi niyyar rarraba kudin domin jari, dama kuma habaka yadda rabon arziki yake a kasar nan.

Za dai a raba kudin ne talakawa su samu, a karon farko tun YouWin, jama'a zasu fara samun jari daga gwamnati.

DUBA WANNAN: Gwamnati na bin diddigi kan batun Kemi Adeosun

Kudaden dai, na daga cikin ma ummul-aba-isin na wahalarda jama'a suka shiga a wancan lokaci, bayan da aka kwashe kudaden aka kaiwa turawa maimakon a barsu a gida arziki ya zaga kowa. Su ko Turawan suka sami jarin juyawa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel