Yanzu Yanzu: Fayose ya fashe da kuka ya ce jami’an yan sanda sun mare shi sannan suka harbe shi (bidiyo)

Yanzu Yanzu: Fayose ya fashe da kuka ya ce jami’an yan sanda sun mare shi sannan suka harbe shi (bidiyo)

Gwamnan jiar Ekiti,Mista Ayodele Fayose, ya ce jami’an yan sanda da aka turo jiharsa don zaben gwamna da za’a yi a rana Asabar sun kai farmaki inda jam’iyyar PD ke gudanar da ganganminta sanna suka ci zarafinsa.

Gwamnan wadda aka gani sanye da wani abun tare wuya ya koro bayanin halin day a shiga sannan ya bukaci magoya bayan jam’iyyar da su jajirce sannan su zabi mataimakinsa wadda shima dan taarar gwamna ne a lemar PDP, Farfesa Olusola Kolapo.

Fayose wadda ya fashe da kuka yayinda yake zantawa da manema laarai ya ce jami’an yan sanda su mare shi sannan suka zungure shi tare da harbin sa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Jami’an tsaro sun tarwatsa magoya bayan PDP daga wajen gangami

Fayose ya kuma bayyana cewa duk abun day a same shi toh babu wanda za’a kama sai sufeto janar na yan sanda.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel