Da dumin sa: Shugaba Buhari ya raba hukumar EFCC gida 2

Da dumin sa: Shugaba Buhari ya raba hukumar EFCC gida 2

Labarin da muke samu da dumin sa na nuni ne da cewa yanzu haka ba da jimawa ba ne shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya rattabawa wata sabuwar doka mai matukar anfani hannu.

Dokar dai wadda take da alaka da binciken kudi ta hanyoyin fasaha da sirri watau Nigeria Financial Intelligence Unit Act (NFIU) yanzu ta samu cikakken goyon baya daga kundin tsarin mulki.

Da dumin sa: Shugaba Buhari ya raba hukumar EFCC gida 2

Da dumin sa: Shugaba Buhari ya raba hukumar EFCC gida 2

KU KARANTA: Rashawa: Atiku yayiwa Buhari wankin babban bargo

Legit.ng ta samu cewa bangaren dake yin aikin wanda a da yake matsayin sashe a hukumar EFCC yanzu zai zama mai cin gashin kansa kenan.

Babban mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin majalisar dattijai Sanata Eta Enag shine ya sanar wa manema labarai dake a fadar shugaban kasa hakan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel