Wani dan sanda da ya sha giya yayi mankas ya hallaka 'yar matar da yake haya a gidanta

Wani dan sanda da ya sha giya yayi mankas ya hallaka 'yar matar da yake haya a gidanta

- Bayan shan giyarsa wani dan sanda ya harbe wata budurwa har lahira

- Dama dai makotan mashayin dan sandan an shaide shi da yawan shan barasa

- Sai dai tuni an kama wannan jami'ain dan sanda son tuhumarsa

Wani sajan din dan sanda wanda ba'a bayyana sunansa ba ya harbe wata budurwa wacce yake haya a gurin mai gidanta.

Wani dan sanda da ya sha giya yayi mankas ya hallaka 'yar matar da yake haya a gidanta

Wani dan sanda da ya sha giya yayi mankas ya hallaka 'yar matar da yake haya a gidanta

Ana zargin dan sandan ne da harbe budurwar mai suna Ikot Ansa akan titin Joseph Nkpang dake cikin birnin Kalaba, lokacin yana cikin mayen giya.

Wani wanda abin ya faru akan gaban idonsa ya bayyana cewa kamar kullum dan sandan ya dawo gida a cikin mayen giya kamar yadda ya saba, jim kadan da dawowar tasa ne gida sai ya dakko bindigarsa kirar gida, ni kuma ina ganin haka ya sa na ruga da gudu domin ya saba irin wannan a duk lokacin da yake cikin mayen giya. Daga nan sai ya yi amfani da bindigar wajen harbar yarinyar a wuyanta da wasu sassa na jikinta.

KU KARANTA: Karar kwana ta kai wani saurayi gamuwa da budurwar da ya hadu da ita a waya

"Ya fara harbe-harbe a sama kamar yadda ya saba, wanda Kuma a lokacin budurwar tana latsa wayarta. sai kawai ya harbeta a wuya, inda ta fadi cikin Jini ta ce ga garinku nan" in ji shaidar gani da idon.

Da aka tuntubi jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Cross-River DSP Irene Ugbo ya tabbatar da faruwar al'amarin, inda ya bayyana cewa wannan laifi ne na kisan kai, kuma tuni rundunar tasu ta kama wanda ya aikata laifin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel